Yakin Duniya: Rikici na nema ya barke tsakanin Amurka da Kasar Koriya ta Arewa
- Yaki na nema ya barke tsakanin Amurka da Kasar Koriya ta Arewa
- Shugaban Amurka yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya hari
- Kwanan nan Koriya ta saki wani mugun makami mai linzami
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya ta Arewa hari don ya taka masu burki wajen makami mai linzamin da su ke harbawa.
Kwanan nan Kasar Koriya ta Arewa ta saki wani mugun makami mai linzami wanda ka iya dura kan Garin Alaska. Amurka tace dole a takawa Koriya burki ko ta karfi da yaji idan ta kama don ta saba doka bayan da ta saki wani mahaukacin makami mai linzami.
KU KARANTA: Gwamnan Arewa ya samar da takin zamani
Amurka tace za ta fi so a zauna yi sulhu amma fa idan abin ya faskara dole Kasar ta tashi tsaye. Kwanan nan dai Koriya ta saki makamin nukiliya da zai iya ratsawa har Kasar Amurka wanda Donald Trump yace ba zai yarda hakan ta faru ba.
Kasar Faransa kamar yadda mu ka samu labari su na shirin daina amfani da duk wani abin hawa da ke aiki da man fetur ko dizil nan da shekarar 2040 kamar yadda wani Ministan kasar ya bayyana.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyo game da abubuwan da su ka faru kwanan nan
Asali: Legit.ng