Kisan Bakassi: Najeriya ta aika wa da jakadan kasar Kamaru takardar sammaci

Kisan Bakassi: Najeriya ta aika wa da jakadan kasar Kamaru takardar sammaci

- Hukumar harkokin wajen Najeriya ta aika wa da jakadan kasar Kamaru takardar sammaci

- Hukumar ta nuna rashin jin dadin ta ga yadda ake kisan yan Najeriya a Bakassi

- Hukumar ta bukaci bayani gamsashe

Hukumar ma'aikatar dake kula da harkokin kasar waje ta Najeriya ta aikawa da jakadan kasar Kamaru a Najeriya Abbas Salahedine da takardar sammaci don ya zo yayi bayani kan zargin kisan da akeyiwa yan Najeriya a tsibirin Bakassi.

Wannan dai yana dauke ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta kuma rarrabawa manema labarai.

Kisan Bakassi: Najeriya ta aika wa da jakadan kasar Kamaru takardar sammaci
Kisan Bakassi: Najeriya ta aika wa da jakadan kasar Kamaru takardar sammaci

Ma'aikatar har ila yau tayi Allah wadai da zancen da takeji na cewa wai yan Najeriyar basu biyan kudin harajin su din kifin da sukeyi shi yasa ake kashe su din.

Legit.ng ta samu labarin cewa a cikin takardar da mai magana da yawun ma'aikatar ta harkokin wajen Najeriya Jane Adams ya sanyawa hannu, ya bukaci kasar ta Kamaru da ta gaggauta ba kasar Najeriya cikakken bayanin abin da ya faru a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng