YANZU YANZU: Jirgin sojin saman Najeriya ya fadi a ciki ruwa
- Jirgin sojin saman Najeriya ya fadi a cikin ruwa
- Baá san ainahin gurin da jirgin ya fada ba a arewa maso gabas
- Babu wanda ya rasa ransa a jirgin
- An kafa kwamitin bincike domin gano inda jirgin ya ke
Wani jirgi mai saukar ungulu Augusta 106 mallakar rundunar sojin saman Najeriya ya hadu da sharrin karfe, sannan ya fada a cikin ruwa wanda baá gano ko ina bane a arewa maso gabas.
Daraktan hulda da jamaá kuma jami’in bayana na hukumar sojin sama, Air Commore Olatokunbo Adesanya, wanda ya tabbatar da faruwar alámarin a ranar Alhamis, yace baá rasa rayuka ba, ya kara da cewa matukin jirgin ne ya sanya jirgin a ruwa domin rage ‘barna.
Majiyarmu ta ce ana nan ana kokari a yanzu domin gano inda jirgin yake.
“A take Shugaban rundunar ya hada kwamitin bincike domin su gano ainahin abun day a haddasa alámarin.
KU KARANTA KUMA: Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – OyegunMatsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun
“Tuni mambobin kwamitin sun isa Maiduguri domin fara aiki,” Inji Adesanya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng