An yankewa wani hukuncin rai-da-rai kan yawaita tusa a masallaci
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani alkalin Kasar Pakistan ya yanke ma wani matashi mai suna Mohammed Al-Wahabi mai shekaru 33 a duniya hukuncin daurin rai-da-rai.
An yanke wa matashin hukuncin ne sakamakon yawan tusa da ya yi har sau 17 a masallatai guda shidda cikin watan Ramadan.
A cewar rahoton, alkalin ya bayyana cewa yawan tusan da dinga yi ya yi sanadiyan da mutane 53 suka bar masallaci a take, a lokacin da ake sahun salla ga mutane da suka halarci masallacin domin yin ibada a wata mai tsarki, don haka ne aka hukuntashi kamar yadda shari’a ta tanadar.
KU KARANTA KUMA: Kalli yadda karamin yaro ke bin bola don neman abunda zai ci (hotuna)
Alkalin kotun ya ba matashin zabi a tsakanin, dauri, yanke masa kai ko kuma jifa. Mai laifin ya bayyana cewa yana fama ne da matsanancin cutar tusa, amma babu wani alkali day a tsaya masa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng