Madalla! An fara sayar da takin zamani a farashi mai rahura a wannan jihar ta Arewa

Madalla! An fara sayar da takin zamani a farashi mai rahura a wannan jihar ta Arewa

An kaddamar da shirin sayar da takin zamani, injunan ban ruwa da galmar shanu a Yola fadar jihar Adamawa, karkashin jagorancin Honarabul Aliyu Wakili Boya shugaban karamar hukumar Fufore tare da kwamishinan ma'aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu Alhaji Mustapha Barkindo.

Mai girma Gwamman jihar Adamawa Bindow Umar Jibrilla shi ya bayar da umarin kaddamar da wannan shiri na sayar da kayan amfanin gona akan farashi mai sauki don manoman jihar su samu saukin aikin noman rani da na damina, a wani bagare na samar musu da damar cin ribar dimukradiyya.

Madalla! An fara sayar da takin zamani a farashi mai rahura a wannan jihar ta Arewa
Madalla! An fara sayar da takin zamani a farashi mai rahura a wannan jihar ta Arewa

Legit.ng ta samu labarin daga majiyar mu ta Zuma Times cewa taron ya samu halartar manyan baki da mukarraban gwamnati.

A jawabin sa Barista Aliyu Wakili Boya ya yi fatan alheri da yi wa jama'a godiya da hadin kai da suka nuna na amsa gayyatar da suka yi.

Daga karshe Gwammna Bindow ya yi godiya ga

wadanda suka shirya wannan shirin don tallafawa manoma, tare da alkawarin cigaba da samar da abubuwan more rayuwa, kamar yadda ya sha alwashi lokacin yakin neman zabe.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel