Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya hana ‘yan siyasa r jihar lika fastoti 'barkatai'

Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya hana ‘yan siyasa r jihar lika fastoti 'barkatai'

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hasssan Dankwambo yayi gargadi da kakkausar murya ga yan siyasar jihar ta Gombe da cewar su guji lika hotunansu a gine-ginen gwamnati da ma wasu sassa na jihar.

Gwamnan yayi wannan gargadi ne a lokacin da mukarraban gwamnatin sa suka ziyarce shi don yimasa gaisuwar sallah a gidan gwamnatin jihar Gombe.

Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya hana ‘yan siyasa r jihar lika fastoti 'barkatai'
Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya hana ‘yan siyasa r jihar lika fastoti 'barkatai'

Legit.ng ta samu labarin cewa Gwamnan ya kara da cewar gwamnati ba zata nade hannu tana kallon ‘yan siyasa suna lika fostoti a gine-ginen gwamnati ba kasancewar yanzu ba lokaci ne na siyasa bane.

Da ga bisani kuma sai Dankwambo ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Gombe da cewar ya tsare duk wani dan siyasar da aka samu da laifin lika fostar takara a cikin jihar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: