Jakadun ƙasashen Turai sun yi hawan Sallah a Kano, kalli hoton a nan
- Jakadun kasashen Turai sun hau daushe a Kano
- Jakadun sun yi hawan ne tare da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi
Sallah biki daya rana, inji Bahaushe, sai dai bukukuwan Sallah basa cika biki musamman a yankin Arewa ba tare da anyi hawan Sallah ba.
Ita dai hawan Sallah al’ada ce ta gidajen masarautun Hausa, inda Sarki da hakimansa ke fitowa bainar jama’a suna masan gaisuwa daga jama’a suma suna mayar da gaisuwa.
KU KARANTA: Muhimman darussa abin lura daga rayuwar marigayi Dan Baba Suntai
Hawan Sallah a birnin Kano ya kan kayatar fiye da na sauran masarautun Arewa, hakan yasa yake samun yan kallo daga ciki da wajen jihar domin kashe kwarkwatar idanunsu.
Sakamakon haka ne jakadan kasar Argentina, Spain dana Denmark suka shiga don jin yadda wannan al’ada mai kayatarwa yake, inda suka yi hawan Daushe tare da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a sallar bana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Legit.ng ta kawo muku hanyoyin magance kamuwa da cuta masassara, kalla
Asali: Legit.ng