Auren sirri: Dokar hana cakuɗa maza da mata a aji na nan tafe a jihar Bauchi

Auren sirri: Dokar hana cakuɗa maza da mata a aji na nan tafe a jihar Bauchi

- Majalisar Dokokin kjihar Bauchi zata hana zaman maza da mata a aji

- Dokar tabbatar da hakan na nan gaban majalisar

Wani kudirin doka dake gaban majalisar dokokin jihar Bauchi a yanzu haka ya janyo rarrabuwar ra’ayi a tsakanin al’ummar jihar.

Dokar na nufin kawo tufkar hanci ga matsalar lalacewar tarbiyya data yawaita a tsakanin daliban makarantun sakandarin jihar, musamman a makarantun dake cakude da samari da yan mata.

KU KARANTA: Jajen mutuwa ga ýan Man Utd: An binne mahaifin Mourinho a mahaifarsa (HOTUNA)

Idan ba’a manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda aka samu wasu dalibai maza da mata dake wata makarantar sakandari a jihar Bauchi, mai suna Sa’adu Zungur Model School suna raba minti, alewa da cingam da sunan suna daura ma kawunansu aure.

Auren sirri: Dokar hana cakuɗa maza da mata a aji na nan tafe a jihar Bauchi
Dalibai maza da mata

Wannan badala ta tayar da hankulan jama’an gari, inda hakan yayi sanadiyyar kulle makarantar da wasu lokutta, inda daga bisani aka bude makarantar.

Sai dai abinda da dan adam, mai wuyar gane hali inji marigayi Dan Maraya, fahimta ta sha bambam a tsakanin jama’an jihar, yayin da wasu ke san barka da zuwan dokar, wasu kuwa sun yi tir da ita.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin zaka mayar da kudi miliyan 100 na tsintuwa?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng