Korar kabilar ibo: Yan sanda na bincike akan masu ingiza samarin arewan
- Yan sanda da sauran jami’an tsaro na bincike akan wadanda ke daure ma samarin arewa gindi akan korar kabilar ibo
- Rahoto daga manyan jami’an tsaro yace an jinkirta kame samarin arewan ne domin bayanen sirri sun nuna masu daure musu gindi sun shirya tada rigima idan an kama su
- Rundunar yan sanda a shirye suke da su kare lafiya da dukiyoyin ibo da ke arewa
Jami’an tsaro dai tuni sun fara bincike akan mutanen da ke ingiza samarin arewa a yunkurin sun a korar kabilar ibo daga arewa.
Jaridar nation ta bada rahoto cewa yan sanda da sauran jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike akan matasan da masu goya musu baya tun shida ga watan Yuni na 2017.
Wata kwakwarar majiya na jami’an tsaro tace kama samarin arewan a wannan lokacin zai iya haifar da babbar fitina, an jinkirta kamen ne domin a kamala bincike akan masu goya musu baya saboda a kashe fitinar daga tushen ta.
“Mun karkatar da akallar binciken namu ne akan mutanen dake daure ma samarin arewan gindi kuma hakar mu tana cin ma ruwa. Bayannan sirin da muka samu ya nuna cewa ana son ayi amfani da kama samarin domin tada fitina a arewacin Najeriya,” Inji wata majiya dake da ke da sani akan binciken.
“Yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kauce ma tarkon masu son tada fitinar da jinkirta kama samarin musamman a cikin watan Ramadan wanda ka iya tunzura mutane wajen tada fitina a arewa.
“Yunkurin samarin arewan na korar kabilar ibo yana da nasaba da siyasa da kuma kabilanci, shi yasa muke kokarin mu gano asalin goya ma samarin baya.
“Mun gano mutane kadan da muke zargi da hannu wajen tunzura samarin arewan.”
Majiyar tace yan sanda suna tsananta bincike akan duka kungiyoyin da ke da hannu cikin yunkurin korar ibon, harda ma iyayen kungiyoyin.
“Tabbas munn san yaran da suka bada sanarwan, kuma ba wai sunfi karfin doka bane. Kawai dai mun jinkirta kama su saboda bayannan sirrin da muka samu
“Zaifi dacewa muyi bincike mu gano masu goya musu baya, wannan zaifi dacewa a halin da muke ciki.
“Mun san abinda ya kamata muyi amma jami’an tsaro suna la’akari da abin da kaiwa-da-kawowa a kasar kafin ta dauki mataki,” Inji majiyar.
Majiyar kuma ta ce rundunar yan sanda ta shirya domin kare lafiya da dukiyoyin kabilar ibo da ke arewa. A lokacin da ya dace mutanen da suka yi yunkurin tada fitina zasu fuskanci hukuncin da ya dace dasu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng