Tattalin arziki: Darajar Dalar Amurka a lokacin Idi
– Babban bankin Najeriya ya saki makudan Daloli a kasuwa
– CBN ya saki Dala Miliyan 240 domin Dala tayi sauki
– Yanzu dai Dalar ba ta wuce N365 ba a kasuwa
CBN na cigaba da sakin Dala domin farashi yayi sauki. Hakan ta sa aka samu saukin Dalar a lokacin bikin Sallah. Sai dai yanzu haka ba mu da labarin farashi a wannan mako.
Kawo yanzu haka Dalar Amurka ta makale a kan N365 yayin da ake bikin karamar sallah. Hakan ya yiwu ne bayan babban bankin Najeriya ya saki makudan Daloli a kasuwa har kusan Dala Miliyan 240.
KU KARANTA: Abin da ke tadawa Dangote hankali
Wani babban Jami’in bankin Isaac Okorafor ne ya tabbatar da wannan bayan a wancan makon babban bankin ya saki wasu sama da Dala Miliyan 830 ga sauran bankuna. Kawo yanzu dai CBN ya saki sama da Dala Biliyan 2.2 domin a samu saukin farashin Dalar Amurka.
Kwanaki wani babban Jami’in CBN ke cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura zuwa karshen shekarar nan. Sanannen abu ne dai cewa Najeriya na cikin matsin tattali kusan tun bayan hawan Shugaba Buhari wanda yanzu abubuwa sun kama hanyar mikewa.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Gobara ta ci wani gida a Abuja [Bidiyo]
Asali: Legit.ng