Kalli yadda Saniya tayi sama sama da wani mutumi a Sakkwato

Kalli yadda Saniya tayi sama sama da wani mutumi a Sakkwato

- Mahaukaciyar Saniya tayi ma wani mutum ɗiban Karen mahaukaciya

- Mutumin yayi yayi ya kufce, amma Saniyar taki

Wani mutum ya tsallake rijiya da baya sa’ilin da wani saniya tayi sama sama da shi, sa’annan tayi wurgu da shi sakamakon baci da ranta yayi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Musulmi ɗan Arewa ya lashe kyautan ɗalibin Likitanci mafi hazaƙa a ƙasar Rasha (HOTUNA)

Wannan lamari ya faru ne a jihar Sakkwato yayin bukukuwan Sallah, inda Sanyar tayi ma mutumin diban Karen mahaukaciya ne da kahonta, sa’annan tayi walagigi da shi, kafin ta buga shu da kasa.

Kalli yadda Saniya tayi sama sama da wani mutumi a Sakkwato
Saniyar da yaron

Cikin wani bidiyo daya watsu a shafukan yanar gizo, an hangi mutumin yana ta kokarin kufcewa daga kahon saniyar, amma ina, hakansa ta gagara cimma ruwa, sakamakon saniyar karfaffa ce.

Kalli bidiyon anan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC ya ake ciki ne?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng