Shirin kiranye: Ba abin da zai hana mu aiki game da Dino Melaye-INEC

Shirin kiranye: Ba abin da zai hana mu aiki game da Dino Melaye-INEC

– Sanata Melaye ya maka Hukumar zabe a Kotu a wancan makon

– Dino Melaye na gudun a tsige sa daga Majalisar Dattawa

– INEC tace ba abin da zai sa ta ja baya daga wannan aikin

Kwanaki INEC ta aikawa Sanata Melaye takarda cewa ya fara shiri. Idan ta tabbata lallai Dino zai bar Majalisar Dattawa babu wata-wata. Sanatan dai ya zura Kotu domin ya ceci kan sa daga wannan yunkuri.

Shirin kiranye: Ba abin da zai hana mu aiki game da Dino Melaye-INEC
Sanata Melaye zai bar Majalisa ba girma ba arziki?

A makon jiya ne Hukumar zabe tace ta samu korafi daga Jama’ar Mazabar Yammacin Kogi na shirin maido Sanata Dino Melaye gida. Tuni dai aka sa rana domin tantance sa hannun Jama’ar domin daukar mataki na gaba.

KU KARANTA: Nnamdi Kanu ya yabi Marigayi Yaradua

Shirin kiranye: Ba abin da zai hana mu aiki game da Dino Melaye-INEC
Dino Melaye ya maka Hukumar zabe a Kotu

Ganin hakan ne ma Sanatan yayi maza ya zura Kotu domin ya tsaida wannan maganar. Sai dai Hukumar zabe na INEC tace ba ta san da maganar Kotu ba kuma ba abin da zai hana ta wannan aiki na ta a yanzu haka.

Kwamishinan Hukumar zabe na Arewa maso tsakiya Mohammed Haruna ya bayyana cewa kwanan nan dai za a fara shirin kada kuri’ar raba gardama da zarar an tantance sa-hannun mutanen mazabar da Sanatan ya ke wakilta.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya auren wanda ku kayi zaman daduro? [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel