Dandalin Kannywood: Na dena fim kuma ban kara auren dan fim ko waye - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Na dena fim kuma ban kara auren dan fim ko waye - Fati Muhammad

- Mutane masu tarin yawa suna ta tambayar ina jarumarsu Fati Muhd ta shiga kwana shekaru kusan tara ba cikakken labarin ta.

- Yawan tambayarne yasa muka cigita nahiyar da jarumar ta shiga akadaina jin koda motsin ta bare maganar ta.

Fati muhammed yar asalin garin Adamawa ce, domin anan aka haifeta aka yaye ta Yola dake Adamawa. Ta fara fim tun tana yar shekara 14 aduniya. ta fara fitowa acikin fina finan hausa tun tana yar shekara 15 aduniya.

Legit.ng ta samu labarin cewa dai tayi aure har sau biyu amma ba wanda ta zauna. Da farko ta auri Jarumi Sani Mai Iska, shekarar su 5 da yin aure suka rabu. Daga nan ta auri Umar Kanu Yayan Mawaki Ali Jita. Shi kuma shekara biyu suka rabu.

Dandalin Kannywood: Na dena fim kuma ban kara auren dan fim ko waye - Fati Muhammad
Dandalin Kannywood: Na dena fim kuma ban kara auren dan fim ko waye - Fati Muhammad

Azantawar Blueprint suka yi da jarumar tace: "Ni yanzu na daina yin fim kuma na daina auren dan fim ko waye domin nayi ban ji da dadi ba. Aurena na yanzu nafi jin dadi dana yi shi. Kuma ina godiya da fatan alkairi ga jaruman yanzu. Ni dai nadaina yin fim. Aure shine mafita ba fim ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng