Mun rage farashin fansan Abubakar daga naira 500,000 zuwa naira 200,000 – Inji Barayinsa a Sokoto

Mun rage farashin fansan Abubakar daga naira 500,000 zuwa naira 200,000 – Inji Barayinsa a Sokoto

- Mutanen da suka sace wani matashi dan kasuwa a jihar Sokoto sun rage kudin fansan da suka nema daga Naira 500,000 zuwa 200,000

- Kwamishanan rundunan ‘yan sanda na jihar Sokoto Mohammed Abdulkadir ya sanar da haka wa manema labarai

Mutanen da suka sace wani matashi dan kasuwa mai suna Abubakar Kakirko a gaban iyalinsa a kauyen Kikirko dake jihar Sokoto sun rage kudin fansan da suka nema daga Naira 500,000 zuwa 200,000.

Kwamishanan rundunan ‘yan sanda na jihar Sokoto Mohammed Abdulkadir ya sanar da haka wa manema labarai a jihar ranar Alhamis.

Ya ce sun sami wadannan bayanai ne bayan iyalan Abubakar sun sanar musu cewa barayin sun yi musu waya don sanar dasu ragin kudin fansa.

KU KARANTA KUMA: Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

Mun rage farashin fansan Abubakar daga naira 500,000 zuwa naira 200,000 – Inji Barayinsa a Sokoto
Mun rage farashin fansan Abubakar daga naira 500,000 zuwa naira 200,000 – Inji Barayinsa a Sokoto

“Mun san cewa ‘yan garkuwan na ajiye da Abubakar a dajin Gundumi wanda ke kan babbar titin Sokoto zuwa Isah.

"Barayin na canza layin wayan tarho amma muna iya kokarin mu domin mu kama su.”

Abdulkadir ya shawarci mazauna jihar da su kai karan duk wanda ko kuma abin daba su yarda da su ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng