Hattara: Ana yi ma Fulani kisan kiyashi a jihar Taraba (HOTUNA)

Hattara: Ana yi ma Fulani kisan kiyashi a jihar Taraba (HOTUNA)

Kabilar Mambilla ta shiga yi ma al’ummar Fulani kisan gilla a karamar hukumar Sardauna na jihar Taraba, haka zalika itama kungiyar Miyatti Allah tayi Allah wadai da wannan hari da ake kai ma Fulani.

Miyatti Allah ta danganta hare haren da nufin karar da al’ummar Fulani gaba daya daga doron kasa. Cikin wata sanarwa data fitara a ranar Laraba 21 ga watan Yuni a garin Jalingo, Miyatti Allah tace an hallaka sama da iyalai 20 a cikin sati daya.

KU KARANTA: Jama’an mazabar Sanata Dino Melaye sun miƙa takardun yi masa kiranye ga hukumar zaɓe

Kungiyar tace a yanzu haka an kashe sama da Fulani mutum 100, da shanu 4000 kuma bawai an daina bane.

Hattara: Ana yi ma Fulani kisan kiyashi a jihar Taraba (HOTUNA)
Rikicin Taraba

Sanarwar data samu sa hannun dattawan kungiyar da suka hada da Alhaji Ahmadu Adamu , Malam Suleiman Musa, Alhaji Hassan Ardo da Alhaji Dauda Jae ta bayyana cewar sama rugan Fulani 180 ne aka kai ma hari a garin Mambilla.

Hattara: Ana yi ma Fulani kisan kiyashi a jihar Taraba (HOTUNA)
Yan gudun hijira

Bugu da kari, kungiyar ta zargi gwamnatin jihar da nuna halin ko in kula ga kisan da ake yi ma Fulanin, don haka ne ma kungiyar ta bukaci mukaddashin shugaban kasa Farfesa Osinbajo daya shigo cikin batun domin shawo kan lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sakamakon rikicin Boko Haram:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: