Mawakan fina finan Hausa na kannywood Abdul Smart zai angon ce
- Fitaccen mawakin fina finan Hausa nan Abdul Smart zai angon ce amaryar sa malama Nana Khadija
- Abdul Smart dai na daya daga cikin yaran gidan Nura M. Inuwa
- A ranar 9 ga watan Yuli 2017 Abdul Smart zai amaryar sa
Fitaccen matashin mawakin fina finan Hausa Abdul Smart zai Angon ce kamar yadda me gidansa Nura M. Inuwa ya angonce.
Mawaki Abdul Smart daya ne daga cikin fitattun matasan mawakan fina finan Hausa na Kannywood, kuma yaro a wurin uban gidansa a harkar waka Nura M. Inuwa.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, mawakin zai angon ce a ranar 9 ga watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki 2017 tare da amaryar sa malama Nana Khadija.

KU KARANTA: Cakwakiya: Tsoho mai shekaru 80 ya memi auren ‘yarshi (Karanta)
Muna taya mawaki Abdul Smart tare da amaryar sa malama Khadija murna tare da yi musu fatan alkhairi, Allah yasa ayi lafiya a tashi lafiya, ya kuma sanya albarka a cikin wannan aure ameen.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wannan matashi mai suna Efe ya lashe gasar BBNaija, ya samu kyautar kudi naira miliyan 25 da kuma motar SUV
Asali: Legit.ng