Kalli yadda wani malamin musulunci ya daure dalibinsa da mari (HOTUNA)
Hotuna sun billon a wani karamin yaro wanda aka ce malamin islamiyar su ne ya daura masa mari a jihar Kaduna.
Legit.ng ta gano cewa wata mai amfani da shafin Facebook Aishat Alubankudi ta yada hotunan wani dalibi a jihar Kaduna wanda aka rahoto cewa malamin Islamiyyar su mai suna Mallam Sufi ya daura masa mari. Ta yi kira ga wgwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai da ya taimaka ya ceci yaron.
KU KARANTA KUMA: Mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba dimokradiyya ba - Tinubu
A cewar ta: “Gwamna Mallam Nasir El-Rufai dan Allah ayi bincike. Wannan rahoto da ba’a tabbatar ba! An tura wannan yaron makarantar Islamiyya a Zaria daga kauyen Boko dake jihar Zamfara.
“Malamin sa ya daure sa da mari sannan kuma ya tura sa yin bara na abincin da zai ci. Sunan Mallamin Sufi, a yankin Rimin Tsiwa dake birnin Zariya jihar Kaduna. Makaranatar Islamiyyar na jikin gidan Alhaji Sani Rimin Tsiwa.
“Wannan na daga cikin tsarin Almajiranci. Babu mamaki yaron ya ji wuya ne sai ya yi yunkurin guduwa don haka ya daura masa mari a lokacin da ya kama shi."
Legit.ng zata sanar da ku halin da yaron ke ciki da zaran an kuma bayar da bayani.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng