Kungiyoyi 3 da Dan wasa Ronaldo zai iya komawa a kakar bana
– Babban Dan wasa Ronaldo na iya tashi daga Real Madrid
– Kungiyar Manchester United na zawarcin Cristiano Ronaldo
– Haka kuma Chelsea da PSG sun tasa Dan wasan a gaba
Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin barin Kungiyar Real Madrid. Mun kawo kadan daga cikin Kulobs din ‘Dan wasan zai iya komawa.
KU KARANTA: FIFA: Za a rage lokacin wasan kwallon kafa
1. Manchester United
Dama kuna da labarin akwai kishin-kishin din cewa Dan wasan yace so yake ya koma Kungiyar sa na da watau Manchester United inda zai kara haduwa da Jose Mourinho.
2. Chelsea
Roman Abromovich mai Kungiyar Chelsea zai dage wajen ganin shi ya dauke Dan wasan na Duniya daga Birnin Madrid zuwa Kungiyar Chelsea da ke Landan maimakon ya koma Manchester.
KU KATANTA: Yadda na yi fama da Ahmed Musa Inji Mahaifiyar sa
3. PSG
Ba mamaki idan Kungiyar PSG ta Faransa ta nemi sayen ‘Dan wasan don kuwa kamar dai Kungiyar Chelsea, Nasir Al-Khelafi yana son ‘Dan wasan kuma yana su na da kudi.
Cristiano Ronaldo na shirin barin Real Madrid bayan an fara zargin sa da kin biyan haraji. Tuni dai irin su Bayern Munchen su kace ba su a wajen zawarcin ‘Dan wasan.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Mai garkuwa da mutane ya zama hamshakin miloniya
Asali: Legit.ng