Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

A ranar Alhamis din da ta gabata ne mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya yi ganawa ta sa’o’i biyu da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Bayan kammala tattaunawar, Sarki Muhammadu Sanusi II bai bayyana wa manema labarai ziyarar mukaddashin shugaban kasar da kuma abubuwan da suka tattauna, sai dai Kamfanin dillancin labarai ta Najeriya NAN ta samo wannan dalilin ziyarar ta Sarki Sanusi daga majiya mai tushe.

NAN ta bayyana cewa Sarki Sanusi ya yi kafa da kafa ne don ya jaddada godiyarsa ga Farfesa Osinbajo bisa saka baki da ya yi wajen tsayar da binciken masarautar Kano da majalisar dokokin jihar ta fara kan zargin masarautar da Sarki da wasu laifuka har guda 8, wanda daga ciki har da yin 'wa kaci ka tashi da dukiyar masarauta'.

Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara
Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

In baku manta ba dai majalisar ta Kano ta dakatar da binciken nata ne sakamakon wata takarda da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya rubuta wa zauren majalisar yana mai hakurkurtar da ‘yan majalisar

Takardar da kakakin majalisar ta Kano, Rayit Honarabul Kabiru Rurum ya karanta a zauren majalisar ta bukaci da majalisar ta Kano da ta dakatar da binciken Sarki da masarauta musamman saboda wasu manyan kasar nan da suka bukaci da a yi hakan

Gwamna Ganduje ya bayyana wa majalisar sunayen wadanda suka nemi gwamnan da ya sanya baki wajen dakatar da binciken wanda cikinsu akwai: Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Shugabannin jam’iyyar APC, Tsofaffin shugabannin Nijeriya, Janar Ibrahim Babangida da Abdussalamu Abubakar, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, manyan ‘yan kasuwa Aliko Dangote da Aminu Dantata

NAN ta tattaro cewa ziyar ta Sarki Sanusi har ila yau na da alaka da batun tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankunan Arewa da na Kudu maso gabashin Najeriya

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng