Mutane 13 da sukafi kowa dadewa a majalisar dokokin tarayya
Jaridar Daily Trust ta tattaro sunayen yan majalisan dookokin tarayya da suka zamar da majalisar tamkar gidan gadonsu yayinda har yanzu aka rasa wanda ya iya tunbukesu a mazabunsu.
Kan gaba a cikinsu shine tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark inda rahotanni sun nuna cewa tun da aka kayar da shi a majalisar, shiru yakeyi tamkar kurma a majalisa.
Ga jerin yan majalisan da sukayi kowa dadewa a gidan:
1. David Alechenu Bonaventure Mark (PDP, Benue, 1999- har ila yau)
An haifesa shekarar 1948, David Mark tsohon soja ne kuma ya zo majalisar a shekarar 1999 karkashin jam’ iyyar PDP.
2. Ahmad Ibrahim Lawan (APC, Yobe, 1999-har ila yau)
Sanata Ahmed Lawan wanda tsohon malami ne haifaffen dan jihar Yobe ne, a rana Litinin din da ya gabata yayi murnan ccikarsa shekaru 18 a majalisa.
3. Nicholas Ebomo Mutu (PDP, Delta, 1999-)
Wannan dan majalisan wakilai da ke wakiltan mazabar Bomadi/Patani a jihar Delta ya shigo majalisa yana dan shekara 39.
4. Ike Ekweremadu (PDP, Enugu, 2003-)
Mataimakin shugaban majalisar dattawa wanda ke wakiltan Enugu ta yamma ya shigo majalisar ne bayan shugabancin karamar hukumar Aninri a jiharsa ta Enugu.
5. Femi Gbajabiamila (APC, Lagos, 2003-)
Dan majalisan mai wakiltar Surulere a jihar Legas ya kasance shugaban masu rinjayen majalisa bayan ya sha kasha a zaben kakakin majalisar a shekarar 2015.
6.Ali Ndume (APC, Borno, 2003-)
Sanata Ali Ndume wanda ya shigo majalisa a matsayin wakilin da karasa majalisar dattawa inda yake wakiltan Borno ta kudu, ya kasance shugaban masu rinjaye a majalisan ne kafin aka tunbukesa sanadiyar rikici da ya samu da shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki da sanata Dino Melaye.
7. James Manager (PDP, Delta, 2003-)
Sanata Manager yana wakiltan jihar Delta ne, ya kasance daya daga cikin wadanda sukafi dadewa a kujerar dan majalisa.
8. Rep Leo Ogor (PDP, Delta, 2003-date)
Leo Okuweh Ogor, wanda yak e a yanzu shugaban maras rijaye a majalisan wakilan tarayya, ya kasance abokin rikicin Gbajabiamila kuma abokin aikinsa.
9. Senator John Owan Enoh (APC, Cross River, 2003-)
10. Senator Philip Tanimu Aduda (PDP, FCT, 2003-)
Yakubu Barde (PDP, Kaduna, 2003-)
Kabiru Marafa Achida (APC, Sokoto, 2003-)
Jagaba Adams Jagaba (1999-2003, 2007-)
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng