Yadda ‘Yar gidan talaka ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Afrika

Yadda ‘Yar gidan talaka ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Afrika

– Ko kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?

– Alakija na cikin matan da su ka fi kowa kudi a tarihin Duniya

– Kwanan ‘Dan ta ya kashe kusan Dala Miliyan 5 wajen auren sa

Folarin Alakija ya watsar da kusan Biliyan 2 wajen bikin aure. Folarin ya auro wata ‘Yar kasar Iran ce da ke zaune a Ingila. Asali Amaryar sa Nazanin ba ‘yar gidan kowa bace.

Yadda ‘Yar gidan talaka ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Afrika
Folarin ya auri wata ‘Yar kasar Iran a fadar Ingila

Folarin Alakija wanda ‘Da ne wajen matar da duk Duniya da wuya a samu bakar mace da ta kera ta dukiya ya auri Nazanin Jafarian Ghaissarifar wata ‘Yar asalin kasar Iran da ke zaune a Kasar Birtaniya. A bikin dai an kashe kudi sama da Naira biliyan 2.

KU KARANTA: Bature ya musulunta a dalilin soyayya da mace

Yadda ‘Yar gidan talaka ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Afrika
Nazanin tayi Digiri kan fannin likitanci da kuma difloma a harkar shari’a

An yi wannan kasaitaccen biki ne a Fadar Blenhim da ke Garin Oxfordshire a Kasar Birtaniya. Asalin Nazanin dai ba masu wadata bane don kuwa Mahaifiyar ta sai da tsiyace ma bayan dawowar su Ingila inda su ke zaune hannun ubangiji.

Shekarun baya dai Mahaifiyar Angon Alakija ta zarce Attaajira Oprah Wimfrey ta Amurka kudi. Alakija mai shekaru 66 ta mallaki sama da Dala Biliyan biyu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ina masu shirin kara tada wani yaki a Najeriya [Ga wani bidiyo]

Asali: Legit.ng

Online view pixel