Bature ya Musulunta sanadiyar soyayya da Musulma kuma a karshe an shafa Fatiha
Michael mai shekara 29 dan asalin kasar Holland, ya hadu da Adin Lubi yar shekara 22 ne, yar kasar Indonesia.
Game da yandda suka hadu, Micheal yace ; “Nayi tunanin zai yi kyau inyi azumin Ramadana da Musulmai. Bayan bincikena a kafafen sada zumunta na yanar gizo, sai na samu Adin kuma na rubuta mata sako.
Abin mamaki, da wuri ta gayyaceni inzo in zauna tare da iyalinsu tsawon kwani 3 a Medan, Indonesia da azumi.
“ Bari ma, sai da nayi makonni 3 a gida. Haka muka fara soyayya da ita.”
“Yawancin masu karban bakoncina a Indonesia da Malaysia Musulmai ne. Basu ta bace mini in Musulunta ba, innama sun nuna min yadda suke rayuwarsu.”
"Dalilin da yasa na zabura kan neman ilimin addinin Musulunci kenan kuma na fara neman ilimi a Masallatan Kuala Lumpur da Jakarta."
KU KARANTA: An kara kudin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
“Yayinda nike zuwa karatu, ban yi niyyan Musulunta ba. Kuma malamai ne sun san da hakan kuma basu damu ba. Bayan makonnin neman ilimi, karatun AlKur’ani da kuma koyan Sallah, sai na fahimci cewa shiga addinin Musulunci ne yafi kyautata a rayuwa na.”
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng