Kamfanin Kannywood ta shirya sakin manyan fina-finai guda 7 da karamar Sallah

Kamfanin Kannywood ta shirya sakin manyan fina-finai guda 7 da karamar Sallah

- Manyan masu shirya fina-finai a masana’antar shirya fina finai ta Kannywood sun shirya fito da fina-finai guda bakwai

- Fim din da za'a fitar sun hada da Rariya, Mansoor, Kanwar Duba rudu, Abu Hassan, Bintoto, Sultana da kuma Munaqisa

Manyan masu shirya fina-finai a masana’antar shirya fina finai ta Kannywood sun shirya fito da wasu daga cikin manyan fina-finan da aka dade ana tsumayi a lokacin shagulgulan sallah karama.

Rahama Sadau za ta fitar da fim din ta mai suna Rariya wanda Yasin Auwal ya bada umarni a ranar 26 ga watan nan.

Fim din Ali Nuhu Mansoor shi ma ana tsammanin zai fito a daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar, haka zalika na Abubakar Mai Shadda Kanwar Duba rudu, wanda Ali Nuhu da Rahama Sadau suka fito a matsayin ya da kanwa.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - JegaBai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Kamfanin Kannywood ta shirya sakin manyan fina-finai guda 7 da karamar Sallah
Kamfanin Kannywood ta shirya sakin manyan fina-finai guda 7 da karamar Sallah

Sai kuma fin din Zaharaddeen Sani Abu Hassan wanda ya bada labarin tabargazar da wata kungiyar ta’addanci ta yi a gari kafin a karshe sojoji su murkushe ta.

Sauran da ake tsammani za su fito a lokacin sun hada da Bintoto, Sultana da Munaqisa

An dai dakatar da fitowar fina finan saboda zagayowar watan Ramadan.

Wannan shi ne karon farko a masana’antar da za a haska manyan fina finai irin wadannan a lokaci daya a sinima.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na Legit.ng TV: Tsakanin maza da mata wa ya fi karya?

Asali: Legit.ng

Online view pixel