LABARI DA DUMI-DUMI: Manjo Al’Mustafa na ganawa da shugaban kungiyar fafutukar Biyafara

LABARI DA DUMI-DUMI: Manjo Al’Mustafa na ganawa da shugaban kungiyar fafutukar Biyafara

- Yanzu haka Manjo Hamza Al’mustafa da shugaban kungiyar MASSOB na ganawa a Kaduna a dakin taron Arewa House

- Ana gudanar da taron ne domin fahimtar juna tsakanin yankunan biyu

- Al-mustafa ya koka cewa kasar Najeriya ta gaji fitina tun yakin basasa

Tsohon babban jamiin mai kula da tsaron lafiyan marigayi shugaba Janar Sani Abacha Manjo Hamza Al’mustafa da shugaban kungiyar fafutukar kafa yankin Biyafara, MASSOB, Cif (Dakta) Ralph Nwazurike na ganawa a halin yanzu kan yadda za a samu zaman lafiya bayan wani wa’adin da wasu kungiyoyin matasan arewa suka ba kabilar Igbo cewa su tattara nasu da nasu su bar yanki nan da watanni 3.

KU KARANTA: Korar Inyamurai: Dan majalisar tarayya daga Kano ya goyi bayan matasan Arewa

Legit.ng ta ruwaito cewa yanzu haka ana gudanar da taron a Kaduna a dakin taron Arewa House domin fahimtar juna tsakanin yankunan biyu bisa dagewa da masu rajin kafa kasar Biyafara keyi da kuma wa’adin sallamar ‘yan kabilar Igbo daga Arewa da wasu kungiyoyin matasan arewa suka bayar.

LABARI DA DUMI-DUMI: Manjo Al’Mustafa na ganawa da shugaban kungiyar fafutukar Biyafara
Tsohon babban jamiin mai kula da tsaron lafiyan marigayi shugaba Janar Sani Abacha Manjo Hamza Al’mustafa

Manjo Al’mustafa wanda ya bada musali da yadda fitina ta gallabi kasar Libya da Sham da Yaman, yace Najeriya ta gaji fitina tun yakin basasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari maganan da Nnamdi Kanu ya yi a kan kafa yankin Biyafara

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng