Duniya kenan: Kar ka so ka ji yadda wani babban Mawakin Duniya ya tsiyace

Duniya kenan: Kar ka so ka ji yadda wani babban Mawakin Duniya ya tsiyace

– Ta karewa babban Mawakin nan Sean Kingston

– Abin da Sean Kingston ya mallaka a Duniya bai wuce $500 ba

– Abin ya kai tare da Mahaifiyar sa yake kwana

Yanzu Sean Kingston bai mallaki gida ko mota a Duniya ba

Mawakin dai ta kai a gidan Uwar sa yake kwana a Amurka

Kingston ya bayyanawa Kotu cewa bai mallaki sama da $500 ba

Duniya kenan: Kar ka so ka ji yadda wani babban Mawakin Duniya ya tsiyace
Duniya juyi-juyi: Sean Kingston ya shiga fatara

Babban Mawakin nan na Kasar Jamaika Sean Kingston ya bayyanawa Kotu cewa ba zai iya biya bashin da wani ke bin sa ba na Dala 12, 500 domin gaba daya abin da ya mallaka a Duniya bai wuce Dala 500.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya ziyarci tsohon Dan wasan kwaikwayo

Sean Kingston
Sean Kingston ya tsiyace bai da ko mota

Mawakin wanda sai da Duniya ta san shi a da can yace shi fa yanzu bai da ko gida guda ko kuma motar hawa. Yake cewa yanzu shi a gidan uwar sa ma yake rabawa a Birnin Los Angeles a Kasar Amurka.

Mun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa wata mata ta rikice yayin da Diyar cikin ta ta buge da auren tsohon Mijin ta. Wannan yarinya dai ta zauna a matsayin agola a gidan wannan mutumi na fiye da shekaru 20.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata 'Yar wasan kwaikwayo ta rasu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng