Wasu ‘Yan matan Najeriya 2 sun shiga tarihi a Duniya
– Wasu ‘Yan Najeriya sun shiga cikin gwarazan Duniya
– Daga cikin wadannan dai akwai wasu mata biyu
– An zabe su cikin sahun 'Yan kasuwa 30 na Duniya
Wasu ‘Yan Najeriya sun yi fice a kaf Duniya
An jero su cikin sahun ‘Yan kasuwan Duniya
Bugu da kari dai wadannan mutane matasa ne
Wasu ‘Yan Najeriya sun shiga sahun mutane 30 ‘yan kasa da shekaru 30 da aka zaba a Duniya da su kayi kaurin suna a harkar kasuwanci. Daga cikin wadannan mutane dai akwai wasu ‘Yan mata har guda biyu.
KU KARANTA: Boko Haram: Osinbajo ya kai ziyara asibitin Maiduguri
Wadannan mutane dai su ne Nasiru ‘Yanmama, Shakeela Tolasade Williams, Mukhtar Onifade, Edikan Udiong da Iyinoluwa Aboyeji. Kamar yadda Jaridar Daily Trust dai ta bayyana daga cikin jerin guda biyu ‘Yan mata ne.
Kuna sane cewa Gwamnatin Buhari ta dage wajen harkar noma a kasar. Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun samu shiga harkar noma ta tsarin nan na babban bankin kasar watau CBN da ke bada rancen kudi domin noma
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi yadda ake fama a Garin Ohuhu
Asali: Legit.ng