Kimanin mutane 20 akayi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna
A ranan Laraba ne, 7 ga watan Yuni akayi garkuwa da fasinjojin mota 20 a titin Abuja zuwa Kaduna da tsakar ranan.
Game da cewar Daily Trust, anyi garkuwa da su ne misalin karfe 12:30 na ranan yayinda wasu yan bindiga suka tare motocin haya kuma sukayi cikin daji da su kusa da kauyen Akilibu.
Daya daga cikin daya daga cikin yan uwan wadanda akayi garkuwa da su ya fadawa jaridar Daily Trust cewa ya samu labarin garkuwan ne ta hanyar wani direban da ya sha da kyar.
Yace kimanin motoci 8 aka tsayar kuma aka fito da dukkan fasinjojin aka kais u cikin daji.
Yace har yanzu masu garkuwa da mutanen basu kira iyalan wadanda akayi garkuwa da suba. “ Direban yace suna tsayar da motocin da ke zuwa daga Abuja tamkar yn fashi.”
“Ya fada mana cewa bayan sun tsaya ne suka lura cewa fasinjojin da ke motocin da ke gabansu basu cikin motocin,”
Wata majiya tace adadin yan bindigan sun kai 30.
KU KARANTA: Gwamnati zata kafa matatar mai a Katsina
Direban yace ya samu daban tsira ne bayan ya roki masu garkuwa da mutanen cewa yana bukatan hutawa a cikin dajin.
Sai masu garkuwa da mutanen suka amince da hakan saboda shekarunsa amma sai ya tsira da kyar.
“Yayinda ya kai kan titi, sai ya ga motara da sauran motocin akan hanya yadda suka barsu. Sai ya koma Abuja kuma ya sanar da iyalan wasu da akayi garkuwa da su.”
Iyalan sunce dai har yanzu ba’a kirasu a waya ba.
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng