Masari azzalumin mutum ne – Ibrahim Shema
Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema yayi watsi da rahoton wata kwamitin bincike sa gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya nada domin binciken gwamnatinsa.
Ya bayyana wannan ne ta mai magana da yawunsa, Oluwabusola Olawale.
Yace: “Abin damuwa ne kuma ba dadin ji ace wata kwamitin bincike sa gwamna Aminu Masari ya nada zatayi watsi da hukuncin kotun daukaka kara da kuma kotun koli sannan ta fara wani aikin sa kai da gwamna Masari ya sata wanda ke nuna zalunci, kama karya, da amfani da kujera wajen sabawa dokar da umurnin kotu.
“Saboda haka muna watsi da wata barazana, rashin adalci, saba doka, da rashin girmama doka kuma ba zamu amince da sakamakon wannan rahoto na zalunci ba.”
Olawale ya nanata cewa kotun daukaka kara ta dakatad da kwamitin saboda Masari bai bi hanyar da ya kamata ba wajen zaben shugaban kwamitin.
KU KARANTA: Aisha Buhari ta dawo Najeriya daga Landan
Ya kira hankalin mutane ga wasikar da Masari ya rubutawa gwamnan jihar Flato, Simon Lalong, a 2016 inda Masari ke bukatan wani alkali ya jagoranci kwamitin.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks
Asali: Legit.ng