Watan Ramadana: Naziru ya saki waƙa, ya koma Tafsiri (bidiyo)

Watan Ramadana: Naziru ya saki waƙa, ya koma Tafsiri (bidiyo)

- Fitaccen mawakin Hausa, Naziru ya zama alaramma

- Naziru na gabatar da Tafseer a Kano

Lallai, ashe haka wata mai alfarma, watan Azumin Ramadana ke sauya halayya da dabi’un mutane? Eh mana, zaka a wannan watan jama’a sun rungumi ibadu ba kakkautawa.

Kwatankwacin yadda ta kasance kenan da shahararren mawakin nan na jihar Kano, wato Nazir Ahmad, wanda ke yi ma kansa kirari da Sarkin waka.

KU KARANTA: Ban ji daɗin yadda Pantami yayi min tayin shiga Musulunci ba – Inji Solomon Dalung

Legit.ng ta samo rahoton Nazirun yana jan baki a wata masallaci dake jihar Kano yayin da wani malami ke gabatar da Tafsirin ayoyin da Nazirun ke karantawa.

Watan Ramadana: Naziru ya saki waƙa, ya koma Tafsiri (bidiyo)
Naziru

Hoton Bidiyon Mawaki Nazir M. Ahmad A Yayin Da Yake Jan Baki A Lokacin Tafsirin Watan Azumin Ramadan.

Ga bidiyon a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda direban Fasto ya musulunta

Asali: Legit.ng

Online view pixel