Mahaukaciya ta haihu a Asaba (HOTUNA)

Mahaukaciya ta haihu a Asaba (HOTUNA)

- Wata mahaukaciya ta haifi lafiyayyen jaririya a Asaba

- Bayan ta haihu lafiya, an dauke ta zuwa asibiti domin ta huta, jaririn na nan cikin koshin lafiya

Wata mahaukaciya ta hafi ‘ya mace a Asaba jihar Delta. Wata mai amfani da shafin Facebook Christian Onwugbolu ta buga hotunan matar da yarinyarta a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni.

Ana yawan ganin matar a gaban wani asibitin tarayya dake Asaba inda a nan ne take yawonta da tsince-tsincen abinci.

KU KARANTA KUMA: Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Wata idan shaida da ta san mahaukaciyar sosai, ta ce suna yawan ganinta a gaban asibitin tarayya dake Asaba inda take yawan neman abinci.

A cewar idon shaidan: “A lokacin da ta samu ciki, Muna ta musu cewa ko dai jkiba ta yi, amma da muka kalli fuskarta sai muka gane cewa ciki ne. yanzu babban tambayar shine wanene ya yi ma mahaukaciya ciki?”

Mahaukaciya ta haihu a Asaba (HOTUNA)
Mahaukaciya ta haihu a Asaba

Ta fada ma Legit.ng cewa matar ta fara nakuda ne a gaban ofishin JAMB dake Asaba sannan kuma mawuyacin halin da mutane suka gani a tattare da ita ne ya sanya sukayi gaggawan garzayawa da ita asibitin FMC sannan kuma a nan ne ta haihu.

Mahaukaciya ta haihu a Asaba (HOTUNA)
Mahaukaciyar da ta haihu

Da ya ke tabbatar da rahoton, jami’in hulda da jama’a na asibitin FMC, Nnamdi Ogbogo, ya fada ma Legit.ng cewa ba’a sallami mahaukaciyar daga asibitin ba. Ya ce har yanzu tana kwance a asibitin, amma baza’a bay an jarida damar ganinta ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel