Aiki yayi kyau: Dala ta yi mugun fadi a kasuwar canji

Aiki yayi kyau: Dala ta yi mugun fadi a kasuwar canji

– Dalar Amurka tayi wani mugun fadi a kasuwar canji

– Naira tayi sama inda Dala ta sha kasa yanzu haka

– Babban bankin kasar na cigaba da dirka Daloli a kasuwa

Dalar Amurka ba ta ji dadi ba kwanan nan

Yanzu haka dai Dalar ta koma N368

Hakan dai na nuna cewa Naira tayi mugun tashi

Aiki yayi kyau: Dala ta yi mugun fadi a kasuwar canji
Naira tayi wani babban yunkuri a kasuwa

Kudin Najeriya watau Naira yayi mugun tashi a kasuwar canji inda ya daga sama yayin da Dalar Amurka kuma ta sha kashi a wannan makon. Dalar dai ta dauki dogon lokacin kimanin makonni 3 a kan N382.

KU KARANTA: An kawo sabuwar haraji domin tara kudin gyara hanyoyi

Aiki yayi kyau: Dala ta yi mugun fadi a kasuwar canji
Gwamnan Babban bankin kasar nan
Asali: Facebook

Yanzu haka dai Naira ta kara daraja har da N14 cikin wannan lokaci. Babban bankin kasar na CBN na cigaba da sakin makudan daloli domin Dalar ta kara sauki. A banki dai ana saida Dalar a kan N305.40.

Kun ji cewa babban bankin kasar na CBN yace kudin kasar wajen Najeriya ya dan kara sauka kasa daga Dala Biliyan 30.52 zuwa Dala biliyan 30.49. Hakan ya nuna cewa kudin kasar ya ja baya da kasa da kashi 1%.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Dalar Amurka za ta taba zama daya da Naira?

Asali: Legit.ng

Online view pixel