‘Shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsayawa takara a zabe mai zuwa’

‘Shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsayawa takara a zabe mai zuwa’

– Wata Kungiya tace Shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsayawa takara

– A cewar ta dole Shugaban ya cigaba da aikin da ya fara na kwarai

– Sai dai har yanzu Shugaban kasar bai da lafiya

‘Yan Kungiyar Buhari Vanguard sun ce Buhari zai kara tsayawa takara

A cewar su Shugaban kasar ya faro aikin gyara

Kungiyar tace akwai bukatar Buhari ya zarce

‘Shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsayawa takara a zabe mai zuwa’
Zaben 2019: Shugaba Buhari zai yi tazarce?

Yayin da Shugaban kasa ke faman jinya wasu na nema ya fito takara domin ya cigaba da irin ayyukan da ya faro na alheri. Kungiyar Buhari Vanguard Musa Aliyu yace su fa su na goyon bayan Shugaban kasar ya kara zarcewa.

KU KARANTA: Gwamnatin nan ta mugaye ce Inji wani Sanata

‘Shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsayawa takara a zabe mai zuwa’
Shugaba Muhammadu Buhari ranar rantsarwa a 2015

A cewar su Shugaban kasar ya cika alkawarin sa na kawo zaman lafiya da kokarin gyara tattalin kasa don hakane matasa ke goyon-bayan sa. Aliyu yace Shugaban kasar ya nuna dattaku wajen mikawa Mataimakin sa mulki yayin da yake fama da ciwo.

Daga hawan Shugaba Buhari zuwa yanzu dai an ga sauyi wajen harkar tsaro. A cewar ‘Global Amnesty Watch’ Sojojin Najeriya na cigaba da samun nasara a filin daga ne a dalilin aiki da gaskiya da kuma sanin aiki na harkar Soji na Shugaban kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 2 da hawan Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel