Babban Dan wasa Ronaldo ya bayyana lokacin da zai bar Real Madrid

Babban Dan wasa Ronaldo ya bayyana lokacin da zai bar Real Madrid

– Babban Dan wasan nan na Real Madrid yace a daina hada sa da Messi

– Cristiano Ronaldo yace babu abin da ke tsakanin sa da Messi sai alheri

– Dan wasan yace zai cigaba da taka leda har ya kai shekara 40

Dan wasa Ronaldo yace har ya kai shekaru 40 yana Real Madrid

Dan wasan yace daga nan kuma zai koma wani Kulob din

Sai dai kuma yace a daina kamanta shi da Dan wasa Messi na Barcelona

Babban Dan wasa Ronaldo ya bayyana lokacin da zai bar Real Madrid
Ba na so ana hada ni da Lionel Messi-Ronaldo

Babban Dan wasan kwallon kafar nan na Real Madrid yace alakar sa da Dan wasa Lionel Messi ta kirki ce, ya kuma kara da cewa kwallon Dan wasan na burge sa don kuwa ya san leda. Sai dai yace bai so ana hada shi don Dan wasan.

KU KARANTA: 'Yar talaka ta ci kyautar miliyoyin kudi

Babban Dan wasa Ronaldo ya bayyana lokacin da zai bar Real Madrid
Manyan 'Yan wasa Ronaldo na Real Madrid da Messi na Barcelona

Dan wasan yace zai cigaba da taka leda har ya kai shekarar 2021, yayin nan ya zarce shekaru 40 zuwa 41 wanda a lokacin ne kwantiragin sa da Kungiyar Real Madrid zai kare. Daga nan kuma Dan wasan yace sai ya nemi wani Kulob din.

Kun san cewa Kungiyar Juventus ta kasar Italiya ta isa zagayen karshe a gasar UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai bayan ta doke Monaco. Juventus za ta kara da Real Madrid a Ranar Asabar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan wuya tayi wuya ya dace mutum ya bar gidan aure?

Asali: Legit.ng

Online view pixel