Goron Ramadan: Abubuwan da ya kamata mai azumi ya nema

Goron Ramadan: Abubuwan da ya kamata mai azumi ya nema

– Yanzu haka dai Musulmai na azumi a fadin Duniya

– Wani masani ya bayyana abin da ya kamaci mai azumi

– Ya kamata a rika samun abinci mai lafiya a wannan wata

Olu Aijotan wani masanin harkar lafiya ya bayyana abin da ya dace mai azumi ya rika ci a wannan wata. Ga dai kadan daga ciki kamar yadda muka tsakuro daga shafin Premium Times:

Goron Ramadan: Abubuwan da ya kamata mai azumi ya nema
Mutane na ibada lokacin azumin Ramadan

1. Shan ruwa

Yana da kyau a fara karya azumi da shan ruwa sai dai kuma ba a son a rika kwankwadar ruwa a lokaci guda wanda hakan yana iya sa ciki ya daure.

KU KARANTA: Za a tsagaita shan sigari a Najeriya

2. Cin ganye da abinci mai gina jiki

Ya fi dacewa mai azumi ya nemi ganye ko kayan marmari yayin buda baki. Irin abin da ake nufi sun hada da kifi, lemu, gwaiba, abarba, ayaba, ganye da sauran su

Goron Ramadan: Abubuwan da ya kamata mai azumi ya nema
Goron Ramadan ga Musulmai masu azumi

3. A guji sukari

Dole mai azumi ya guji abubuwa irin su sukari da ice cream ko sinadarin soda. Irin wadannan sinadarai na kara nauyi don haka dole a guje su a cikin watan Ramadan.

A takaice dai ba a son cin abinci mai nauyi yayin azumi kuma ana bukatar a rika motsa jikin kafin ayi buda baki wannan zai kara lafiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata 'Yar wasa ta bayyana alakar ta da Sanata Dino Melaye

Asali: Legit.ng

Online view pixel