ABIN AL'AJABI: Wata aya ta bayyana a kabarin Sharifiya Hajiya Halimatu Sheik Sidi Attahiru Sakkwato

ABIN AL'AJABI: Wata aya ta bayyana a kabarin Sharifiya Hajiya Halimatu Sheik Sidi Attahiru Sakkwato

- Ruwan sama da aka tafke a Sakkwato ta rubde wasu kaburbura a wani makabarta

- Kabarin marigayia Hajiya Halima Sidi Attahiru na cikin kaburburar da suka rubda

- An tara da ita Hajiya Halima Sidi Attahiru lafiya kalau kamar yanzu aka sanyata cikin kabari da kuma wata likkafaninta fari kal tare da ita

Yara marigayia Hajiya Halima Sidi Attahiru sun shaida cewa: “A ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu a garin Sakkwato mun je makabarta domin mu yi addu'a ga mahaifiyarmu wato Hajiya Halima Sidi Attahiru. Muna zuwa makabartar, sai muka iske mutane maza da mata cike da mamaki. Sakamakon yadda ruwan sama da aka yi a kwanaki biyu da suka gabata ya rubde wasu kaburbura a makabartar.

Cikin kaburburar da suka rubda harda kabarin wannan baiwar Allah, inda aka tarar da ita lafiya kalau kamar yanzu aka sanyata cikin kabarin. An sami likkafaninta fari kal, babu ko datti a jikinsa, yadda ka san kamar yanzu aka siyo shi daga kasuwa. Jiikinta kuwa kamar yanzu aka sanyata cikin kabari.

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Rariya cewar mutanen da suka taru a wurin sun tsaya cike da mamaki saboda yadda yanzu shekaru 2 ke nan da rasuwa.

ABIN AL'AJABI: Wata aya ta bayyana a kabarin Sharifiya Hajiya Halimatu Sheik Sidi Attahiru Sakkwato
Sharifiya Hajiya Halimatu Sheik Sidi Attahiru Sakkwato

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na daf da fara koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan uwa

Ita dai wannan Sharifiya, wacce aka fi sani da Hajiya 'Yar Dubu, ta kasance Uwargidan Sheikh Sidi Attahiru Sakkwato ce, kuma sun yi rayuwa a tare fiye da shekaru 50. Har ya zuwa lokacin rasuwarsa, Hajiya Halima ta kasance mai kyawawan dab'iu a rayuwarta, kuma tana da yawan hakuri. Sannan an shaideta da tsayuwa akan gaskiya da kuma fada da zalunci a cikin kowane irin hali. Kullum burinta ta kasance tare da raunana wadanda aka zalunta. Har wala yau sam bata son rayuwa tare da zalunci ko da kuwa makusantan ta ne.

Acewar wanda ya bada labarin: “Ni da ke wannan rubutu, ganau nake ba jiyau ba, domin kafin a gyara Kabarin na ga komai da idanu na kuma akwai bidiyon.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Asali: Legit.ng

Online view pixel