Jerin kudin jirgin hajjin bana na kowani jiha – Daga NAHCON

Jerin kudin jirgin hajjin bana na kowani jiha – Daga NAHCON

Maniyyata aikin hajji daga Najeriya zasu akalla N1,500,000 kafin su sami daman sauke babban rukunin musulunci bana.

Zuwa yanzu, hukumar kula da ayyukan Hajji ta Najeriya ta wato NAHCON ta fitar da jerin kudaden jihohi 22 cikin 36 na kasar.

Mafi karancin farashin shi ne N1,480,000 wanda maniyyatan jihar Katsina zasu biya. Maniyyatan jihar Oyo sune zasu biya farashi mafi yawa na Naira 1,584,069.

A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, da kuma N1,145,998.92 ga masu masu babbar kujera.

Jerin kudin jirgin hajjin bana na kowani jiha – Daga NAHCON
Jerin kudin jirgin hajjin bana na kowani jiha – Daga NAHCON

A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.

KU KARANTA: An mika yan matan Chibok ga ministan Buhari

Ga jerin kudaden da maniyyata daga Najeriya zasu biya:

Nasarawa:1,544,894.16

Niger:1,525,483.30

Kaduna:1,535,503.68

Kano:1,537,859.97

Katsina: 1,498,502.70

Adamawa:1,530,101.18

Yobe:1,520,101.18

Kano:1,537,859.97

FCT:1,538,218.62

Bauchi:1,523,122.41

Plateau:1,529,036.80

Zamfara:1,510,461.65

Sokoto:1,524,618.90

Gombe:1,516,118.90

Benue:1,522,118.90

Kebbi:1,534,659.85

Taraba:1,521,138.21

Osun:1,548,153.42

Armed Forces:1,538,379.22

Ogun:1,561,943.97

Anambra:1,511,173.77

Kwara:1,501,571.27

Ekiti:1,525,191.27

Edo:1,551,331.87.

Oyo:1,584,069.02.

Ban da wadannan kudaden, akwai Naira 38,000 na hadaya da kowane maniyyaci zai biya daga aljihunsa a Makkah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng