Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano (HOTUNA)

Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano (HOTUNA)

- Sabuwar amarya ta sanya ma mijinta da itama kanta wuta

- Matar ta zargi mijinta da aikata fasikanci kafin ta cinna ma kanta da mijin wuta

- An yi gaggawan kai mijin nata asibiti bayan an tsinkayi yana da sauran numfashi

Wata sabuwar amarya ta cinna ma kanta da mijinta wuta kan zargin fasikanci a jihar Kano.

Legit.ng ta tattaro cewa mummunan al’amarin ya faru ne a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, da misalin karfe goma sha biyu na tsakar dare (12:00am) a yankin Sabon Gari dake jihar Kano.

An tattaro cewa matar na zargin mijinta da fasikanci bayan ta jiyo hirar da ya wakana tsakanin sa da wata mata da ba’a san ko wacece ba.

Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano (HOTUNA)
Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano

A cewar jaridar The Punch, matar da ta fusata da mijinta ta cinna wuta a kan wani galan din man fetur wanda a take ya tashi sannan kuma ya kone gidansu.

KU KARANTA KUMA: Ka yi mun gani, sai dai...: ‘Yan adawa sun yabawa Shugaban kasa Buhari

An rahoto cewa matar wacce ta kone fiye da tunani ta mutu a take a gurin yayinda akayi gaggawan kai mijin nata asibiti inda anan shima ya bi ta daga baya.

Wani idon shaida, Emmanuel Okorie, ya yi bayanin cewa anyi auren matar wacce ke dauke da juna biyu ga mijin nata makonni biyar da suka shige.

Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano (HOTUNA)
Amarya ta sanya ma kanta da mijinta wuta a jihar Kano (HOTUNA)

A cewar Okorie, mijin wanda aka ambata da suna Emeka ya bayyana mai cewan mahaifiyarsa ce ta tursasa shi auren matar tasa.

Amma dai, Okorie ya kasa tabbatarwa ko hiran wayar ne ya yi sanadiyan faruwar mummunan al’amarin.

Kakakin yan sandan jihar Kano, Musa Magaji Majiya, ya bayyana cewa hukumar yan sanda ta kaddamar da wani bincike don gano sanadin faruwar al’amarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ya dace abokiyar zaman ka ta duba maka sakonninka na wayar salula?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: