Mata ta guntulewa mijinta mazakuta saboda yana neman mata
Wata mata a kasar Thailand ta guntulewa mijinta azzakari sannan ta sha maganan kwari ta kashe kanta, yan sanda sun bada rahoto ranan Talata.
Kawinnart Saezong,mai shekara 33 ta mutu ne ranan Litinin a asibitin Phayao, ta hallaka kanta ne bayan ta guntilewa mijinta azzakari yayinda yake bacci ranan asabar bayan ta samu labarin yana lalata a waje.
Amma mijin mai suna Niran Saewang, ya tsira. An kaishi asibitin Lampang inda aka mayar masa da azzakarinsa, wani jami’in asibiti ya tabbatar da hakan.
Jami’an asibitin sun samu dukan azzakarinsa da ta guntule sannan suka daskarar da shi da kankara kafin aka mayar da shi.
Wannan bashi bane lokaci na farko da asibitin ke kula da irin wannan matsala kuma sun kasance suna samun nasara.
KU KARANTA: Dangote zai noma shinkafa a arewacin Najeriya
Asibitin tace Niran na samun sauki a asibitin amma likitoci sun bayyana cewa zai iya fitsari amma ba zai sake iya jima’I ba.
Asali: Legit.ng