Jaruma Nafisa Abdullahi ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu

Jaruma Nafisa Abdullahi ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu

- Jaruma Nafisa Abdullahi ta kai tallafi na farko ga kauyen Gurguzo da ke karamar hukumar Igabi a jahar Kaduna a karkashin sabuwar gidauniyar ta mai suna ‘Love Laugh Foundation’.

- Sabuwar gidauniyar wacce ta kaddamar a makon da ya gabata na da zummar tallafawa gajiyayyu, mabukata da marayu ta hanyar raba masu kayan abinci da na masarufi da zai rage masu zafin talauci.

Legit.ng ta samu labarin cewa Nafisa ta bayyana cewa ta fara da wannan kauyen ne saboda rahoto da ta samu na irin matsalolin da mutanen kuayen ke fuskanta musamman na rashin abinci. A fadarta, lokaci ya yi da ya kamata mutane irinsu su fara taimakawa jama’a ta hanyoyin da suke ganin za su iya.

Ta ce, “A duk lokacin da mutum ya kai matsayin da jama’a suke kaunarsa, musamman dan fim da yake alfahari da jama’a, kasancewar su ne ke siyan finafinan da yake fitowa a ciki. Ya dace ya dauki matakin bin hanyoyin da zai tallafawa al’umma, ya samu lada a wajen ubangiji”.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu
Jaruma Nafisa Abdullahi ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu

Ta ziyarci kauyen ne tare da jarumi Abdul M. Shareef da Sulaiman Sir Zeesu wadanda duk suka yabawa namijin kokarinta kuma suka gode da kasancewa da ita yayin da ta ke wannan aikin alkhairi.

Al’ummar kauyen wadanda aka tallafawa da shinkafa, taliya da sauran kayan masarufi sun bayyana farin cikin su bisa sha tara ta arziki da jaruma Nafisa ta yi musu, sun kuma yi kuma mata godiya da addu’ar Allah ya karfafa mata gwiwa ta ci gaba da yin ayyukan alkhairi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng