Kunji babbar ta'asar da wasu shugabannin kananan hukumonin Kano ke tafkawa
Yayin da wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44 ke karewa a ranar litinin mai zuwa, Fulani makiyaya na ci gaba da kokawa dangane da yadda shugabannin ke sayar da Burtalai da filin kiwo a sassa daban daban. Fulanin dai sun bukaci gwamnatin jihar ta sanya baki domin kare yanayin rikici tsakanin Fulani da Manoma.
Rahotani daga kananan hukumomin Tudun wada, da Kibiya da Bagwai da kuma Gezawa, na nuna yadda Fulanin ke damuwa game da yadda shugabanin wadannan kananan hukumomi dake baring ado suka tsaga makiyaya a yankunansu kuma suka sayar ga manoma, yayin da a wasu bangarorin kuma aka sayarda burtalai da makiyaya ke wucewa da dabbobinsu ga ‘yan kasuwa da sauran jama’ar gari.
Legit.ng ta samu labarin cewa Alhaji Ahmad Canji Mangari,shugaban reshen ihar Kano, na kungiyar Fulani makiyaya ta GABDAN, yace abinda ya kyautu shine Gwamnatin ta maida burtalolin da aka sayardawa manoma da sauran jama’a, idan dai ana son a kyautatawa makiyaya da kuma wanzuwar zaman lafiya tsakanin bangarori biyu.
Ya kara da cewa makiyayun a halin yanzu na bukatar kari amma a maimakon kari sai gashi wasu shugabanin kananan hukumomi na sayarda wanda ake neman Kari akai.
Kwamishinan ma’aikatar Gona da Albarkatun kasa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, yace matakin da aka dauka shine duk inda aka je aka tsaga ko domin gona ko filin gidan mai ko kuma domin gina wani shago, Gwamna ya bada Umarni cewa dole duk wata takarda sai ta biyo ta gabansa.
Ya kuma baiwa makiyaya tabbacin cewa dukkan wani wuri da aka ce za a ci burtali ko filin kiwo yana kan doka kuma wannan dokar zata yi aiki akan ko wanene.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng