Kundin Kannywood: Yan iska sun sassari jarumi Ahlan Sheriff da adda

Kundin Kannywood: Yan iska sun sassari jarumi Ahlan Sheriff da adda

Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan daba ne, sun Sassari fitaccen dan was Ahlan da adda a gefen goshin sa, da gadon bayan sa. Sanadiyya wannan sara da aka yi masa, Ahlan ya samu mummunan rauni, wanda tuni aka sallame shi daga asibiti.

Wannan hari da aka kai masa, ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda Nasir Gwangwazo, fitaccen masubucin labaran finafinan Hausa ya bayyana wa majiyar mu. Kokarin samun Ahlan a waya bai yiwu ba, domin ta na kasha. Sai dai kuma Gwamgwazo ya ce a zaman yanzu Ahlan ya na gida, kuma ya na samun sauki.

Legit.ng ta samu labarin cewa shahararren dan fim kuma furodusa ne, wanda ya yi fice wajen iya fitowa a matsayin mai zabga Turanci gangariya a finafinan Hausa.

Kundin Kannywood: Yan iska sun sassari jarumi Ahlan Sheriff da adda
Kundin Kannywood: Yan iska sun sassari jarumi Ahlan Sheriff da adda

Kuma a zaman yanzu an rage ganin sa cikin ‘yan fim, saboda ya fi maida hankali ga aikin sa na koyarwa da ya ke yi a Kwalejin Ilmi Mai Zurfi ta Sa’adatu Rimi, da ke Na’ibawa, Kano.

Kadan daga cikin finafinan da ya yi, sun hada da: Jinsee, 419, Mafiya da Gadon Baya da sauran su.

An kai masa harin ne a unguwar Kabuga Janbulo in da yake Zaune.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng