An yi Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano
- An gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin
- Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin Kano
An gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin, 22 ga watan Mayu.
Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin Kano.
KU KARANTA KUMA: Matan Chibok: Wani Sanata ya bayyana abin da ya sa aka yi musanya da ‘Yan ta’adda
Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 89 a duniya, ta kuma rasu ta bar jikoki goma sha biyar a duniya.
Ta rasu bayan shekaru 34 da rasuwar mijinta Malam Aminu Kano shahararen dan siyasa a arewacin Najeriya wanda ya kafa jam’iyyar NEPU ta masu ra’ayin rikau na yan mazan jiya.
Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kamar maza.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
An saki 'Yan matan makarantar Chibok da aka sace shekaru ukku da ya gabata
Asali: Legit.ng