Masu siyar da kwado na ciniki sosai yanzu a Jigawa
- Masu siyar da kwado na ciniki sosai a Hadejia, jihar Jigawa, Najeriya
- Kwado iri-iri ne sannan kuma ba ko wanne ake ci ba, kamar yadda wasu na dauke da guba mai hatsari
- Masu kasuwanci a kasuwa sun bayyana sana’ar a matsayin garabasa ta fannin habbakan kasuwa
Masu siyar da kwado na ciniki sosai a Hadejia sakamakon yawan neman dabban da akeyi, a cewar rahotanni.
Kwado iri-iri ne sannan kuma ba ko wanne ake ci ba, kamar yadda wasu na dauke da guba mai hatsari.
Koda dai bai kasance abincin da arewa ke yawan ta’ammali da shi ba, amma ana yawan amfani da shi a wasu garuruwa dake yankin kudancin kasar.
Wani bincike da akayi a kasuwar Hadejia ya nuna cewa masu siyar da kwado na ciniki sosai sakamakon bukatar dabbar da ya yawaita a jihar.
KU KARANTA KUMA: Ba za ta sabu ba: Shugaba Buhari yayi nadi ‘Yan Majalisa sun ce da sake
Ana siyar da wani babban sanda wanda ke dauke da kwadi guda 20 a kan naira dubu daya (1000) sannan kuma karamin sanda dauke da kananan kwadi 10 a kan naira dari hudu da amshin (450).
Masu sana’ar sun bayyana cinikin a matsayin garabasa ta fannin ci gaban kasuwancin.
Alhaji Haruna Shuaibu, wani mai kasuwancin kwado, ya bayyana cewa yana ciniki sosai saboda yawan bukatar kwado da akeyi.
Shuaibu yayi bayanin cewa bukatar dabban ya fi karfin wanda suke samar wa, ya kara da cewa dabba na da karanci a lokacin da ruwa bai fara sauka ba.
Zakari Hadi, wani mafaraucin kwado, ya bayyana cewa yana samun tsakanin N2000 da N3000 daga sana’ar kwado, ya kara da cewa wannan ya bashi damar dauke duk wani bukatun sa ta fannin kudi.
Hadi ya bayyana cewa yana sanya tarko sannan ya kama kwadi, ya kara da cewa dabbobin na da yawa a yankin.
Ya yi bayanin cewa kwadi iri daban-daban ne, wanda aka rarrabe su zuwa wanda ke da guba da kuma mara guba.
Ya ce farautar kwado na da wahala saboda akwai wasu fasaha da mutun yake bukata da zai basa damar gane irin kwado da zai kama.
KU KARANTA KUMA: Musulunci bai yarda da barace barace ba, inji mai alfarma Sarkin Musulmi
Wani mai sana’ar, Mista Sam Akiboh, ya bayyana cewa yana zuwa kasuwar daga Benue don ya siya kwadi.
Akiboh ya ce ana yawan bukatar dabbar a yankin sa saboda dadin sa sannan kuma ga saukin farashi.
“Ina samun riba na kimanin N20, 000 daga sana’ar kwado duk sati.”
Sunyi kira ga gwamnati da ta yi abunda ya kamata don karfafa noman kwado.
Legit.ng ta ruwaito cewa jihar Kebbi na da daya daga cikin manyan kasuwannin albasa a Najeriya.
Kasuwar wacce ke a karamar hukumar Yauri ta samar wa matasa ba adadi ayyukan yi.
A halin da ake ciki yan Najeriya na ci gaba da maida martani ga al’amarin kasar.
Kalli wannan bidiyo na Legit.ng a kasa:
Asali: Legit.ng