Alhamdulillah! Naira ta cigaba da samun galaba a kasuwan bayan fagge
- Naira ta kara daraja zuwa N380 ga dalar Amurka a kasuwan bayan fagge
- Amma ta samu nuksani ga Fam inda aka tashi kasuwa N490 sabanin N485
- Kuma ta zauna daram dam a N420 ga Yuro
Kudin Najeriya Naira na cigaba da samun galaba akan dalar Amurka a kasuwan bayan fagge.
Game da cewan rahotanni, Naira ta kara darajan ne zuwa N380 ga dala sabanin N385.
Amma ta samu nuksani ga Fam inda aka tashi kasuwa N490 sabanin N485, kuma ta zauna daram dam a N420 ga Yuro.
Wannan abu na faruwa ne bayan babban bankin Najeria CBN ta yawaita dalar Amurka cikin kasuwa.
KU KARANTA: An damke barayi cikin jirgin sama
Jaridar Legit.ng ta bada rahoton cewa CBN ta saki kudi $457.3m cikin kasuwan canji.
Kana kuma Naira ta kwana a 305.60 a kasuwan banki.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng