Kaji abunda 'yayan marigayi Ado sukace game da tsomomuwar da Sarki Sanusi ke ciki
- Sakamakon rahotannin dake yaduwa na cewa kawunan 'ya'yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya rabu a dalilin rabon kudin gado da kuma matsalolin da ba a rasawa na cikin gida
- Wasu daga cikin 'ya'yan marigayi sun musunta batun
- Inda suka bayyana cewa kawunansu a hade yake babu wata rashin fahimta dake tsakaninsu duk da yawan da suke da shi.
Daya daga cikin 'yan marigayi Sarkin, wanda ya yi magana a madadin iyalan gidan marigayi Ado Bayero, wanda kuma ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa wasu ne kawai daga wajen masarautar Kano ke naman raba kansu amma babu wani rabuwan kai da ya shiga tsakaninsu a dalilin rabon gado ko kuma batun mukamin sarauta.
KU KARANTA: Za'a fara tatsar man fetur daga rake
Dan gidan Sarkin ya kuma kara da cewa iyalan marigayi Ado Bayero sun dauki Sarki Sanusi II tamkar uba a wajensu domin dan uwansu ne na jini. Kuma a hannun mahaifinsu ya tashi, haka kuma yana auren daya daga cikin 'yar marigayi Sariki, wato Sadiya Ado Bayero.
Legit.ng ta samu daga shafin Rariya cewa don haka ne ya yi fatan Allah ya kara hada kansu, tare da kare su daga masu neman raba kawunansu.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng