Yaki da sata: Ka ji wani shiri da Sanatocin Najeriya ke yi

Yaki da sata: Ka ji wani shiri da Sanatocin Najeriya ke yi

– Majalisa za ta tabbatar da wani kudiri a watan 7

– Kudirin nan na tona asirin barayi zai zama dokar kasar

– Hakan zai taimaka wajen yaki da sata a Najeriya

Magu ya bayyana cewa EFCC na bankado makudan kudi sanadiyar sabon tsarin nan.

Tsarin na tona asiri-ka samu rabon ka yana aiki ainun.

Majalisa tace ta kusa shigar da shi cikin dokokin kasar.

Yaki da sata: Ka ji wani shiri da Sanatocin Najeriya ke yi
Magu na EFCC na bankado makudan kudi

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace nan da dan lokacin Majalisa za ta gama aiki kan kudirin da aka kawo mata na tonon asiri. Idan har kudirin ya shiga cikin dokokin kasar zai taimaka wajen yaki da sata kwarai.

KU KARANTA: EFCC ta kara damke wani tsohon Gwamna

Yaki da sata: Ka ji wani shiri da Sanatocin Najeriya ke yi
Shugaban Sanatocin Najeriya Bukola Saraki

Haka kuma akwai wasu kudirori da shugaban kasa ya aiko wanda sun dade a Majalisar da Dr. Bukola Saraki yace za ayi kokari domin tabbatar da su. Hakan zai sa sata ya rasa gindin zama a kasar.

Kasar Ingila tace an saci sama da Dala Biliyan 480 daga 1960 zuwa yanzu Gidan tarihin nan na Afrika watau Chatham House yayi wannan nazari. Jakadan kasar Birtaniya yace sata da cin hanci ne ke kashe Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An tasa wani Sanatan Anambra a gaba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng