An fara binciken badakalar daukan ma'aikata aiki a DSS

An fara binciken badakalar daukan ma'aikata aiki a DSS

- Hankalin jama'a yayi kacokan, kan badakalar yadda aka kwashi 'yan arewa aiki a hukumar 'yan sandan ciki ta SS.

- Mutan kudu sun koka ganin jihohin su ba'a basu kaso mai tsoka ba, kamar takwarorinsu na arewa.

- Masu kare sabgar, sunce ramuwa ce ake yi wa jihohin Arewa, saboda shekara da shekaru, mutan arewa sun fuskanci wariya, wajen daukarsu aikin na tsaro.

Majalisar dattijai ta Najeria, ta fara sauraren korafi na cewa an yi aringizo na ma'aikatan hukumar tsaron farin kaya ta DSS, inda wasu jihohin na arewa suka sami dozin dozin na wakilci, jihohin kudanci kuwa, suka tashi da wakilci mitsil, wanda hakan ya kawo shakku da zargin bangaraqnci, wanda dama yayi wa Najeria katutu a harkokin raba mukamai.

Kwamitin kula da harkokin Federal Character, karkashin Sanata Tijjani Kaura, ya ce zasu yi gaggawar fitar da sakamako na bincikensu.

KU KARANTA KUMA: Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

An fara binciken badakalar daukan ma'aikata aiki a DSS.
An fara binciken badakalar daukan ma'aikata aiki a DSS.

An dai ruwaito cewa, Jihar Kano da Katsina sun sami kujera kusan 60 a sabbin daukar na ma'aikatar, amma jiha kamar Akwa Ibom ta tashi da mutum biyar kacal.

Za a tuna wannan batu idan aka duba shafukan sada zumunta na Legit.ng da ke faceebook da twitter.

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Yadda mu ka yi da Buhari Inji Femi Fani-Kayode

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng