Gwamnatin jihar Barno ta dakatar da rufe sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar

Gwamnatin jihar Barno ta dakatar da rufe sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar

- Gwamnatin jihar Borno ta dakatar da shawarar da ta dauka na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira saboda burbudin ayyukan Boko Haram da har yanzu jihar ke dan fama da su

- Gwamnan jihar Kashim Shettima ya fadi hakan ne a bukin mika wa jihar gudunmuwar wasu gine-gine da gidauniyar ‘Victims Support Fund VSF’ ta yi a garin Bama ranar Talata

-Ya kara da cewa duk da haka za su ci gaba da aikin gina wuraren da suka lalace sanadiyyar hare-haren Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace gwamnatin jihar ta dakatar da shawarar da ta dauka na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira saboda burbudin aiyukkan Boko Haram da har yanzu jihar ke dan fama da su.

Ya fadi hakan ne a bukin mika wa jihar gudunmuwar wasu gine-gine da gidauniyar ‘Victims Support Fund VSF’ ta yi a garin Bama ranar Talata.

Gwamnan ya ce gwamnati ta amince da shawarar dakatar rufe sansanonin ne kamar yadda ada ta shirya saboda kira da shawarwarin da jami’an tsaro suka bata da ta dada jinkirtawa tukuna.

Gwamnatin jihar Barno ta dakatar da rufe sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar
Gwamnatin jihar Barno ta dakatar da rufe sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar

“Idan mutane suka koma garuruwansu ya kamata ace rayuwarsu ta koma kamar yadda take da ne wanda tabbaci da samun haka ya rataya a kan mu ne”.

KU KARANTA KUMA: Wata 'yar Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram

Kashim Shettima ya kara da cewa duk da haka za su ci gaba da aikin gina wuraren da suka lalace sanadiyyar hare-haren Boko Haram. Ya kuma godewa gidauniyar kan gudunmuwar da take ba jihar.

Ya ce a shekarar 2015 gidauniyar ta ba jihar gudumawar kayayyakin gini da ya kai Naira miliyan 250 domin gina wuraren da za su amfani mutanen jihar.

Daga karshe mataimakin gidauniyar VSF Tijjani Tumsa ya ce gidauniyar za ta ci gaba da tallafa wa jihar da irin wadannan taimako.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin Najeriya ta ce wata yarinya daga cikin 'yan matan Chibok da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram ta tsere daga hannun kungiyar.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ne ya tabbatar wa da faruwan hakan, inda mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar minsitoci a ranar Laraba.

An yi amannar cewa wasu sojoji ne suka tsince ta a lokacin da tsere tana hanyar guduwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubuwa sun canza bayan dawowar Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: