Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya

Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya

- Sheikh Bala Lau, ya jinjina wa gwamnan inda yace zaman lafiya ba karamin abu bane a cikin al'umma

- Simon Lalong ya nuna farincikin sa da ziyarar Sheikh Abdullahi Bala Lau jihar Filato

Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa Ikamatis Sunnah Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jinjina wa gwamnan jihar Plateau Rt. Hon. Simon Bako Lalong bisa kokarin sa na tabbatar da zaman lafiya a jihar, inji rahoton Rariya.

Sheikh Bala Lau ya bayyana haka ne yayin wata rangadi daya kai jihar tare da shuwagabannin kungiyar, a loakcin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan a gidan gwamnatin jihar ta Filato.

KU KARANTA: Yan sara-suka su 11 sun gamu da fushin wata kotu a jihar Bauchi

A yayin jawbain Sheikh Bala Lau, ya jinjina wa gwamnan inda yace zaman lafiya ba karamin abu bane a cikin al'umma.

Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya
Sheikh Bala tare da gwamnan Filato

Shehin Malamin yace abin farinciki ne kwarai ace yanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokarin kawo zaman lafiya haka shima gwamnan yana nasa kokarin a matakin jiharsa.

"Shakaru biyu zuwa uku da suka wuce, jihar Plateau ta kasance jiha da take fama da tarzoma wanda munin abun ya kai kowa na tsoron ya shigo jihar. Anyi fama da kashe-kashe. An zubar da jini, an kone dukiya.

Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya
Sheikh Bala Lau yayin dayake jawabi

"Amma cikin ikon Allah, tun da Allah ya kawo wannan gwamna sai ga abubuwa suna sauyawa. Wannan kuma shine yake nuna sha'awar da yake dashi ga zaman lafiya. Babu abunda yakai zaman lafiya. Ko ita kadai aka samu a gwamnati to an samu ribar democradiyya," Inji Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Legit.ng ta ruwaito Sheikh Lau yayi godiya ga gwamnan bisa ziyarar ta'aziyya da ya kai har gidan Marigayi Sheikh Dr. Alhassan Sa'id ga iyalan Malamin.

Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya
Gwamnan Filato Lalong na jawabi

A nasa jawabin, gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya nuna farincikin sa da ziyarar Sheikh Abdullahi Bala Lau jihar Filato inda yace babu shakka ziyarar tasu zata bada gudunmawa wajen kara dankon zumunci da zaman lafiya.

Bugu da kari gwamnan yace addu'o'in jama'a ne da kuma ikon Allah suka tabbatar da zaman lafiyar da ake gani a jihar.

Sheikh Bala Lau ya jinjina ma gwamnan Filato bisa tabbatar da zaman lafiya
Tawagar malaman Izala tare da gwamnan Filato

Daga karshe gwamna Lalong yayi godiya ga Sheikh Abdullahi Bala Lau da tawagar sa, kuma yayi fatan Allah ya mayar dasu gida lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda yan bindiga suka harbe yaron makauniya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng