Dan Usama bin Laden yayi barazana ga kasar Amurka kan kisan mahaifinsa
- Dan Usama bin Laden, Hamza yayi barazana ga kasar Amurka kan kisan babansa
- Wasikun da aka samu a harin da aka kace mahaifinsa ya nuna cewa Hamza na shirin daukan fansa
Game da rahotannin yan jarida, dan gidan Usama, Hamza yana neman fansa akan kisan mahaifinsa da akayi kuma da alaman shi zai zama sabon shugaban Al-Qaeda.
Tsohon ma’aikacin hukumar FBI, Ali Soufan, yayinda yake magana da gidan talabijin CBC a wata hira cewa: "Ya fada masaa cewa… yana tuna komai…ko murmushin da ka bani…dukkan abinda ka fada mini.”
Ali Soufan yace Hamza na kalon kansa wani abu. Lokacin da yake karami, mahaifinsa na sanyasa a cikin bidiyo rike da bindiga.
KU KARANTA: Ba abinda ya samu shugaba Buhari - Garba Shehu
Soufan yace sabon maganar Hamza da ya fito, yayi jawabai tamkar mahaifinsa, kalamai da maganganun da mahaifinsa yayi amfani da shi.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng